Acts 18

A Korinti

1Bayan haka, Bulus ya bar Atens ya tafi Korinti. 2A can ya sadu da wani Bayahude mai suna Akwila, ɗan garin Fontus, wanda ya zo ba da daɗewa ba daga Italiya tare da matarsa Firiskila, domin Kalaudiyus ya umarci dukan Yahudawa su bar Roma. Sai Bulus ya tafi yǎ gan su, 3da yake shi ma mai ɗinkin tenti ne kamarsu, sai ya zauna ya yi aiki tare da su. 4Kowace Asabbaci kuwa yakan yi muhawwara a majamiʼa, yana ƙoƙari yǎ rinjayi Yahudawa da Helenawa.

5Saʼad da Sila da Timoti suka iso daga Makidoniya, sai Bulus ya ba da kansa ga yin waʼazi kaɗai, yana tabbatar wa Yahudawa cewa Yesu shi ne Kiristi. 6Amma saʼad da Yahudawa suka yi hamayya da Bulus suka kuma shiga zaginsa, sai ya karkaɗe tufafinsa a cikin rashin yarda, ya ce musu, “Alhakinku yana a kanku! Ba ni da wani laifi. Daga yanzu zan tafi wajen Alʼummai.”

7Sai Bulus ya bar majamiʼar ya kuma tafi ƙofar da take kusa da gidan Titiyus Yustus, mai yi wa Allah sujada. 8Kiribus, shugaban majamiʼa, da dukan iyalinsa suka gaskata Ubangiji; Korintiyawa masu yawa kuwa da suka ji shi suka gaskata, aka kuwa yi musu baftisma.

9Wata rana da daddare, Ubangiji ya yi magana da Bulus a cikin wahayi ya ce: “Kada ka ji tsoro; ka ci gaba da yin magana, kada ka yi shiru. 10Gama ina tare da kai, ba kuma wanda zai fāɗa maka ya cuce ka, domin ina da mutane da yawa a wannan birni.” 11Saboda haka Bulus ya zauna a nan har shekara ɗaya da rabi, yana koya musu maganar Allah.

12Yayinda Galliyo yake maƙaddas Akayya, Yahudawa suka haɗa kai suka tasar wa Bulus, suka kuwa kawo shi cikin kotu. 13Suka yi zarge cewa, “Wannan mutum yana rarrashin mutane su yi wa Allah sujada a hanyoyin da suka saɓa wa doka.”

14A daidai saʼad da Bulus yana shirin yin magana, sai Galliyo ya ce wa Yahudawan, “Da a ce ku Yahudawa kuna gunaguni game da munafunci, ko kuma wani babban laifi, da sai in iya sauraronku. 15Amma da yake ya shafi gardama ce game da kalmomi da sunaye da kuma dokarku-sai ku ji da ita da kanku. Ni ba zan zama mai shariʼa kan irin waɗannan abubuwa ba.” 16Saboda haka ya sa aka kore su daga kotun. 17Sai duk suka juya kan Sostenes shugaban majamiʼa suka yi masa dūka a gaban kotun. Amma Galliyo ko yǎ kula.

Firiskila, Akwila da Afollos

18Bulus kuwa ya ci gaba da zama a Korinti na ʼyan kwanaki. Saʼan nan ya bar ʼyanʼuwa ya shiga jirgin ruwa zuwa Suriya tare da Firiskila da Akwila. Kafin ya tashi, ya aske kansa a Kenkireya saboda alkawarin da ya yi. 19Suka isa Afisa, inda Bulus ya bar Firiskila da Akwila. Shi kansa ya shiga majamiʼa ya kuma yi muhawwara da Yahudawa. 20Saʼad da suka roƙe shi ya ƙara ʼyan kwanaki da su, bai yarda ba. 21Amma da yake barin wurin, ya yi alkawari cewa, “Zan dawo in Allah ya yarda.” Saʼan nan ya tashi daga Afisa a jirgin ruwa. 22Saʼad da ya sauka a Kaisariya, sai ya haura ya gai da ikkilisiya saʼan nan ya gangara zuwa Antiyok.

23Bayan ya yi ʼyan kwanaki a Antiyok, Bulus ya tashi daga can ya zaga koʼina a yankin Galatiya da Firjiya, yana ƙarfafa dukan almajirai.

24Ana cikin haka sai wani Bayahude mai suna Afollos, ɗan ƙasar Alekzandariya, ya zo Afisa. Shi masani ne, yana da cikakken sani na Nassosi. 25An horar da shi a hanyar Ubangiji, ya kuma himma ƙwarai a magana, ya kuma yi koyarwa game da Yesu, daidai, ko da yake baftismar Yohanna ce kaɗai ya sani. 26Sai ya fara magana gabagaɗi a majamiʼa. Saʼad da Firiskila da Akwila suka ji shi, sai suka gayyace shi gidansu suka ƙara bayyana masa hanyar Allah sosai.

27Saʼad da Afollos ya so ya tafi Akayya, sai ʼyanʼuwa suka ƙarfafa shi suka kuma rubuta wa almajiran da suke can da su marabce shi. Da isowarsa, ya zama da taimako ƙwarai ga waɗanda ta wurin alheri suka gaskata. 28Gama da ƙwazo ya ƙaryata Yahudawa a muhawwara a fili, yana tabbatar daga Nassosi cewa Yesu shi ne Kiristi.

Copyright information for HauSRK